Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang na tabbatar da wadatar abinci yayin da musulmai ke bikin babbar sallah
2020-08-01 16:09:51        cri
Hukumomi a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin, sun yi kokarin tabbatar da wadatar abinci da dabbobi yayin da musulmai ke bikin babbar sallah.

A cewar Song Yajun, mataimakin magajin garin Urumqi, yayin bikin, hukumomin birnin za su yanka sa da raguna 1,700 a kowace rana, sama da rabin adadin da aka saba yankawa a kullum, tare da kaji 33,000, wanda shi ma ya karu da kaso 30.

Haka zalika, hukumomin birnin za su tabbatar da samar da kimanin ton 1,000 na kayan lambu da ton 260 na madara da kuma ton 120 na kwai a kullum.

Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da jihar Xinjiang ke fuskantar bazuwar cutar COVID-19 tun daga tsakiyar watan da ya gabata.

Yayin da ake fama da annobar COVID-19, galibin mazauna birnin Urumqi sun soke gudanar da tarukan iyali, inda suka zabi su kasance a gida domin dakile yaduwar cutar.

A ranar Laraba, hukumomi suka fara gudanar da shirin samar da nama ga zauna birnin kan matsakaicin farashi, inda suka shirya samar da ton 200 na naman rago da ton 150 na naman sa, zuwa ranar 12 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China