Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan bankuna fiye da 70 sun fara ajiyar kudin Sin RMB
2020-08-15 16:37:00        cri
Babban bankin kasar Sin ya sanar da wani rahoto a jiya Juma'a, dangane da yadda ake amfani da kudin Sin RMB a kasashe daban daban a bana. Inda aka ce ya zuwa yanzu wasu manyan bankuna ko kuma hukumomi masu kula da harkokin kudi na kasashe daban daban fiye da 70 sun fara maida kudin Sin RMB cikin kudin musanya da suke ajiyarsu a gida.

Rahoton ya ambaci yanayin amfani da kudin Sin RMB tsakanin kasa da kasa a shekarar 2019, inda yawan kudin RMB da bankunan kasashe daban daban suka yi amfani da su a bara ya kai Yuan trilian 19.67, wanda ya karu da kashi 24.1% bisa makamancin lokacin shekarar 2018.

Zuwa karshen shekarar 2019, babban bankin kasar Sin ya kulla yarjeniyoyin musayar kudi tare da manyan bankuna ko kuma hukumomin kudi na kasashe da yankuna kimanin 39, ta yadda wannan tsari ya shafi wasu manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki, gami da tattalin arzikin dake tasowa cikin sauri. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China