Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaru: Kasashen kungiyar EU sun cimma matsaya kan bude kan iyaka
2020-06-28 18:12:08        cri
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun ruwaito a jiya Asabar cewa, bisa la'aikari da samun ci gaba a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19 a nahiyar Turai, da sauran kasashe, mambobin kungiyar tarayyar Turai EU sun cimma matsaya kan bude kan iyakokinsu ga wasu kasashe fiye da 10, amma ban da kasar Amurka.

Kafofin watsa labarun da suka hada da Reuters, da jaridar New Youk Times, da dai sauransu, sun ce kungiyar EU na shirin bude kan iyakokinta ga kasashen irinsu Japan, da Koriya ta Kudu, da Canada, da Austriliya, da New Zealand, da dai sauransu, daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa. Sai dai zuwa yanzu kungiyar EU ba ta sanar da hakan a hukumance ba, saboda shirin na jiran samun zartaswa daga dukkan mambobin kungiyar.

An ce, dalilin da ya sa kasar Amurka bata cikin jerin sunayen kasashen da ake shirin bude iyakokin gare su shi ne, domin kungiyar EU ba ta da gamsuwa game da yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka. Inda a cewar jaridar Washington Post ta kasar Amurka, matakin da ake shirin dauka ya nuna ra'ayin kungiyar EU cewar, kasar Amurka ta gaza a yunkurinta na hana yaduwar annobar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China