Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan ganin bangarori daban daban sun nuna goyon baya ga WHO
2020-08-11 20:31:36        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin na fatan ganin kasashen duniya za su tsaya kan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban masu fada a ji a duniya, da nuna goyon baya ga hukumar lafiya ta duniya WHO, don ta ci gaba da taka rawar jagoranci, a hadin gwiwar da kasashen duniya ke yi don dakile cutar COVID-19.

Rahotanni sun nuna cewa, bayan da Amurka ta janye jiki daga hukumar WHO, tana ci gaba da neman yin tasiri a muhawarar da kungiyar G7 za ta yi, don neman gyaran fuska ga hukumar, lamarin da ya sanya wasu manyan kasashen Turai janyewa daga muhawarar.

Dangane da hakan, jami'in na kasar Sin ya ce, ba wanda zai iya maye gurbin hukumar WHO, a aikinta na jagorantar yaki da cutar COVID-19, ta la'akari da matsayin hukumar na mafi karfin fada a ji, da yawan kwararru a fannin kiwon lafiyar jama'ar duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China