Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: JKS na daukar lamurran jama'a da matukar muhimmanci
2020-08-11 20:04:13        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta a yau Talata cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na nacewa manufarta, ta daukaka matsayin rayuka, da moriyar jama'ar kasar, sa'an nan tarihi zai shaida kokarin da gwamnatin kasar take yi a fannin tinkarar annobar COVID-19, gami da nasarorin da ta samu.

Wadannan abubuwa a cewar kakakin, sun sha bamban da ra'ayin da jam'iyyun kasar Amurka ke kai, na mai da mafi yawan hankali kan moriya a fannin siyasa.

Rahotanni sun nuna cewa, wasu wakilan kafar watsa labaru ta NBC ta kasar Amurka, sun samu izinin shiga cikin cibiyar nazarin kananan kwayoyin halittu ta birnin Wuhan na kasar Sin, don yin intabiyu. To amma a cewar kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Morgan Ortagus, wai wakilan NBC ba su mayar da hankali ga neman bayanai na gaskiya ba, kuma a cewar sa jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, na kokarin kare kanta ne daga jin kunya, maimakon ceton rayukan jama'a.

Game da zargin da mista Ortagus ya yi, Zhao Lijian ya ce, masu nazarin kimiya da fasaha na kasar Sin, sun riga sun yi cikakken bayani kan tsarin da ake bi wajen kula da cibiyar nazarin kwayoyin halittu ta Wuhan, da yadda ake gudanar da nazari a cibiyar na bisa tsari, ga manema labaru. Kaza lika ba a samu wata shaidar da za ta goyi bayan zargin da wasu mutane suke yi, cewa wai cibiyar ce asalin cutar COVID-19 ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China