Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yukurin Ta Da Yakin Cacar Baki A Duniya Ba Zai Yi Nasara Ba
2020-08-07 15:19:11        cri

Yayin da kasashe daban daban ke kokarin tinkarar annobar cutar COVID-19, da neman farfado da tattalin arziki, wasu 'yan siyasa na kasar Amurka suna ci gaba da yunkurin ta da rikici, da wani yanayi na kiyaya a duniyarmu. Misali, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, a kwanakin baya ya tafi kasashen Birtaniya da Denmark, don neman lallashinsu don su hada gwiwa da kasar Amurka a kokarinta na matsawa kasar Sin lamba, sa'an nan mista Pompeo ya tuntubi kasar Indiya, don neman sanya kasar ta daina hadin kai da kasar Sin a fannin masana'antu. Daga bisani, bayan da Mista Pompeo ya koma kasar Amurka, ya yi wani jawabi, inda ya kara shafa wa jam'iyyar mai mulki ta kasar Sin, wato JKS, kashin kaza. Wato yana kokarin baza ra'ayi na kallon kasar Sin a matsayin wata barazana ga duniya, da jaddada bambancin ra'ayin siyasa, da kokarin janyo sauran kasashe cikin yunkurinsa na matsawa kasar Sin lamba, da neman wani sabon zagayen yakin cacar baki a duniya.

Ma iya cewa wannan tunani na neman yakin cacar baki ya riga ya zama wani muhimmin ra'ayi cikin manufofin kasar Amurka a fannin harkar diplomasiyya. Ko da yake, Amurkawa fiye da dubu 150 sun riga sun mutu sakamakon bazuwar cutar COVID-19 a kasar, amma 'yan siyasa na kasar ba su taba daina matsawa kasar Sin lamba ba, har ma suna ta kokarin tsaurara matakansu.

Abubuwan da suka yi sun hada da yin amfani da annobar COVID-19 wajen dora wa kasar Sin laifi, da shafa mata kashin kaza; da neman bata huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, ta hanyar yada jita-jitar cewa kasar Sin za ta sanya kasashen Afirka tsunduma cikin tarko na karbar bashi, da wai Sinawa na cin zarafin 'yan Afirka. Wadannan 'yan siyasa na kasar Amurka suna kokarin ta da rikici a yankin teku na Nanhai na kasar Sin, da neman sanya wasu kasashen dake yankin yin taho-mu-gama da kasar Sin; da yunkurin bata sunan tsarin siyasa na kasar Sin, da lalata huldar hadin kai dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. A takaice, ma iya cewa wadannan 'yan siyasa na kasar Amurka na neman mai da kasar Sin saniyar ware a duniya.

Dalilin da ya sa suke yin haka ya shafi bangarori daban daban: Saboda an kasa shawo kan bazuwar cutar COVID-19 a kasar Amurka, don haka ana neman dora laifi ga kasar Sin. Sa'an nan ana neman yin tasiri kan babban zaben kasar dake karatowa, ta hanyar nuna karfi yayin da ake kula da al'amuran kasa da kasa. Ban da wannan kuma, ana neman hana ci gaban kasar Sin, don kare matsayin kasar Amurka na samun cikakken fin karfi a duniya.

Bayan samun barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta samu shawo kan bazuwar cutar cikin kankanin lokaci, sa'an nan tattalin arzikinta na farfadowa cikin sauri, lamarin da ya kara daukaka matsayin kasar a idanun mutanen duniya. Hakan ya sa wasu 'yan siyasan kasar Amurka damuwa sosai, har ma sun fara tilastawa sauran kasashe yin zabi a tsakanin kasashen Sin da Amurka, don neman mai da kasar Sin saniyar ware. Sai dai wannan mataki ba zai yi amfani ba, saboda ya sabawa tunanin mutane na wannan zamani.

Ma iya cewa, wadannan 'yan siyasa na Amurka sun yi girman kai, inda ba su san ainihin yanayin da kasarsu ke ciki ba. Kasar Amurka ta yanzu ta yi watsi da ra'ayi na kasancewar bangarori da yawa a duniya, da ciniki cikin 'yanci, inda take kokarin daukar matakai bisa kashin kanta, da danna sauran kasashe yadda ta ga dama, ba tare da lura da dokokin kasa da kasa ba, hakan ya sa mutanen kasashe daban daban ke kin amincewa da ita.

Bayan da annobar COVID-10 ta barke a kasar Amurka, maimakon neman hadin gwiwa da sauran kasashe don daidaita wannan matsala, kasar ta yi kokarin dawo da kamfanoni da jari cikin kasuwanni na gida, bisa son kanta. Maimakon nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa, Amurka ta janye jiki daga hukumar lafiya ta duniya WHO, da shafa bakin fenti ga kungiyar ciniki ta duniya WTO, lamarin da ya sanya ake fuskantar wani mawuyacin hali a fannin kulawa da al'amuran kasa da kasa. Wannan kasar da ba ta da adalci ko kadan, sauran kasashe, idan suna da sanin ya kamata, da dogaro a kansu, za su yarda su ci gaba da nuna mata goyon baya? Hakika jaridar the Guardians ta kasar Birtaniya ta riga ta wallafa wani sharhin cewa, bayan da aka samu lalacewar yanayin bazuwar cutar COVID-19, da gagarumar zanga-zangar kin yarda da nuna bambancin launin fata, a kasar Amurka, galibin jama'ar kasashen Turai sun daina nuna amincewa ga wannan kasa.

Har ila yau, wadannan 'yan siyasan kasar Amurka ba su fahimci kasar Sin ba. Wani muhimmin dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arziki shi ne turbar tsarin siyasa na gurguzu mai salon musamman na kasar Sin da ta zaba. Saboda haka kasar Sin ba za ta zama tambar kasar Amurka ba, wato ba za ta dauki tsarin siyasa na kasar Amurka ba. Duk da haka, kasar Sin ba ta da niyyar yin taho-mu-gama da kasar Amurka. Sai dai ba za ta yarda a dinga lalata moriyarta ba. Ya kamata mu lura da cewa, wani babban burin da kasar Sin ta sanya a gaba, shi ne kyautata zaman rayuwar jama'arta, da ciyar da zaman al'ummar kasar gaba, gami da kare zaman lafiya a duniya. Saboda haka, manufar ta da yakin cacar baki da kasar Sin, da wasu 'yan siyasan kasar Amurka ke dauka, mataki ne mai cike da kuskure, wanda ba shi da gaskiya ko kadan.

Idan mun dubi manufofin kasar Sin, za mu ga yadda kasar take kokarin bude kofarta ga duniya, da neman tabbatar da moriyar kowa yayin da take hadin gwiwa da sauran kasashe. Kasar Sin na taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya, inda gudunmowar da ta samar ta kai kashin 30% cikin karuwar tattalin arzikin duniyarmu. Tana kuma tallafawa kokarin rage talauci a duniya, inda gudunmowar da ta samar a wannan fanni ta zarce kashi 70% a duniya.

A fannin dakile yaduwar cutar COVID-19, kasar Sin ta dauki wani matakin jin kai mafi girma a tarihi, inda ta yi alkawarin samar da kudin tallafi dala biliyan 2 ga sauran kasashe, da mai da allurar rigakafin da kasar za ta samar a matsayin wani maganin da ake yin amfani da shi don kare lafiyar jama'ar kasashe daban daban, da kara samar da tallafi ga kasashen dake nahiyar Afirka. Wannan kasa, dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, da taimakawa sauran kasashe, me ya sa ba a son hadin gwiwa da ita?

A wannan zamanin da muke ciki, mutanen duniya sun rungumi ra'ayi na kare zaman lafiya, da hadin gwiwa da juna. Don haka idan ana son sake ta da yakin cacar baki, da mai da wata kasa saniyar ware, to, hakan shi ne mayar da hannun agogo baya. Hakika, kasar Sin wadda take kokarin aiwatar da manufar "Ziri Daya da Hanya Daya", don karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe, tare da neman ciyar da tattalin arizkinsu tare, ba wata kasa ce da za a iya kebe ta a wani bangare, ko kuma mai da ita saniyar ware ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China