Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kira bikin hada hadar ba da hidima na kasa da kasa na shekarar 2020 a watan Satumba mai zuwa
2020-08-10 20:02:39        cri

Kwanan baya, an kira taron kungiyar 'yan kasuwar kasashen ketare, da taron gabatarwa na kamfanoni masu jarin waje, na babban bikin hada hadar ba da hidima na kasa da kasa na shekarar 2020.

Rahotanni sun nuna cewa, a watan Satumba mai zuwa, za a kira bikin a nan birnin Beijing ta kafar Intanet, da kuma a cibiyar taron kasar Sin dake nan Beijing, bisa jigon "Ba da hidima a duniya da kawo moriya ga juna". Taron zai shafi ayyukan ba da hidima dake da alaka da fasahar 5G, da na'urori masu sarrafa kansu, da dai sauran fasahohi na zamani.

Ya zuwa ran 3 ga watan nan, kamfanoni 898 sun tabbatar da za su shiga taron ta Intanet, kana 1,217 sun tabbatar za su halarci taron da za a yi a cibiyar taron kasar Sin dake nan Beijing. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China