Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hada hadar shige da ficen hajoji ta Sin ta bunkasa a watan Yuni
2020-07-14 19:41:36        cri

Tsakanin wa'adin shekara guda, zuwa watan Yunin bana, alkaluman hada hadar shige da ficen hajoji na kasar Sin sun karu da kaso 5.1 bisa dari, inda alkaluman kayan da kasar ta fitar ya karu da kaso 4.3 bisa dari, yayin da na wadanda ta shigo da su ya karu da kaso 6.2 bisa dari.

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce, kasar ta samu bunkasar hada hadar cinikayyar waje, sama da abun da aka yi tsammani a watanni 6 na farkon shekarar nan.

A cewar hukumar, cinikayyar hajoji a kasuwannin ketare ta ragu da kaso 3.2 bisa dari cikin shekara guda a rabin shekarar, da yawan kudin da suka kai yuan tiriliyan 14.24, kwatankwacin dalar Amurka Tiriliyan 2, wanda hakan ke nuna saukar alkaluman da kaso 1.7, idan an kwatanta da raguwar da aka gani cikin watanni 5 na farkon shekarar.

Kaza lika hukumar ta kwastam, ta ce duk da yanayin tangal tangal na kasuwanni da aka gamu da shi a rubu'in farko na shekarar, a rubu'i na biyu an ga alamun farfadowa, da ci gaba da daidaito, a fannin hada hadar shige da ficen hajoji a kasar, yayin da fannin fitar da hajoji ke kara bunkasa cikin watanni 3 a jere. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China