2020-08-10 10:42:35 cri |
A cewar cibiyar CSSE, ya zuwa karfe 9:36 na safiyar ranar Lahadi agogon Amurka, yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar, ya karu zuwa miliyan 5,000,603, kana yawan wadanda cutar ta halaka ya kai 162,441.
Wani hasashe da cibiyar kula da harkokin kiwon lafiya da kididdiga (IHME) a jami'ar Washington, ta yi na nuna cewa, nan da ranar 1 ga watan Disamba dake tafe, cutar za ta halaka mutane da yawansu ya kai 295,011 a kasar.
A game da batun samar da alluran riga kafin cutar COVID-19 kuwa, darektan cibiyar cututtuka masu yaduwa ta Amurka, kana mamba a kwamitin yaki da cutar COVID-19 ta fadar White House Dr. Antthony Fauci, ya bayyana cewa, sakamakon gwajin allura da aka yi kan dabbobi da bil-Adama, sun nuna cewa, akwai tabbacin za a samar da riga kafin da ba shi da wani hadari kuma mai inganci, nan da karshen wannan shekara ko farkon shekara mai zuwa.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China