2020-08-09 16:49:36 cri |
Wei Shangjin, wani shehun malami mai nazarin hada-hadar kudi da tattalin arziki dake aiki a jami'ar Columbia ta kasar Amurka, ya ce yadda ake neman tilasta a sayar da kamfanin TikTok da wani farashi mai rahusa ga wani kamfanin kasar Amurka zai iya haifar da hadari ga kamfanonin kasar Amurka da yawa, wadanda ke zuba jari a kasar Sin.
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bada umarni, inda ya hana kamfanonin kasar Amurka mu'amala da kamfanin ByteDance na kasar Sin, wanda ke mallakar TikTok a halin yanzu, cikin kwanaki 45.
Cikin wannan umarnin da shugaban Trump ya bayar, ya ce an taba sauke APP din TikTok har fiye da karo miliyan 175 a kasar Amurka, gami da fiye da karo biliyan 1 a duk duniya. Yana zargin APP din da satan bayanan masu yin amfani da shi, lamarin da a cewarsa zai haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China