Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya zama wajibi a kare nau'in bakar kasa
2020-07-23 11:28:28        cri

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin kare nau'in bakar kasa samfurin chernozem da ake da ita a lardin Jilin, dake arewa maso gabashin kasar ta Sin.


Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, lokacin da yake rangadi a gundumar Lishu ta birnin Siping, inda ya ganewa idanun sa yankin gwaji, na kyautata yanayin kasa nau'in chernozem, da yadda ake noman masara, a wani bangare na ziyarar sa a lardin na Jilin.


Arewa maso gabashin kasar Sin, daya ne daga yankunan duniya 3 da ke da nau'in kasar chernozem, yankin da aka fi noma masara da waken soya, kuma bakar kasar dake yankin na samar da yabanya mai yawan gaske, sai dai kuma yabanyar yankin na raguwa, sakamakon raguwar nagartar sinadaran kasar.


Shugaba Xi ya ce, dabarar mayar da karmamin masara zuwa gonaki domin kare saiwoyin tsirrai, na taimakawa wajen bunkasa sinadarai masu amfani dake cikin kasa, da tabbatar da danshin kasa, baya ga kare tsirrai daga zaizayar kasa, sakamakon tasirin iska ko ruwa. Matakin da a cewar shugaban na Sin ya dace a dora muhimmanci wajen kara aiwatar da shi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China