2020-06-18 13:11:17 cri |
Bayan taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya yi bayani kan sakamakon da aka cimma a wannan taro.
Ya ce, mahalarta taron sun yi musayar ra'ayoyi kan goyon bayan kasashen Afirka game da yaki da cutar, da kuma karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da ma sauran kasashen duniya wajen yaki da cutar, inda suka cimma matsaya kan manyan batutuwan da abin ya shafa. An gabatar da sanarwar hadin gwiwa ta wannan taro, wadda ta bayyana matsayin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka kan wasu manyan batutuwa.
Chen Xiaodong ya kara da cewa, an gudanar da wannan taro a lokacin da ya dace, taron zai yi muhimmin tasiri ga kasa da kasa. Da farko, zai inganta hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar yaki da cutar COVID-19, sa'annan, ya nuna zamunci mai karfi dake tsakanin Sin da Afirka. A karshe dai, zai karfafa aniyar kasa da kasa don cimma nasarar yaki da annobar cikin sauri. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China