![]() |
|
2020-07-09 10:28:20 cri |
Jakada Liao Liqiang, ya bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani ta kafar bidiyo da ya gudana a jiya Laraba, inda ya ce kawo yanzu, kwararru a fannin aiki likita na Sin, sun gudanar da tarukan karawa juna sani har guda 8 tare da takwarorinsu na Masar. Kaza lika Sin na fatan dorewar musayar ra'ayi, da gudanar da shawarwari, da hadin gwiwa ta kafofin zamani, a fannin samarwa, da kuma amfani da alluran rigakafin cutar da hadin kan Masar.
Kalaman na Mr. Liao na zuwa ne, 'yan kwanaki bayan gudanar da taro karo na 9 na dandalin ministocin Sin da na kasashen Larabawa ko CASCF a takaice, wanda shi ma aka gudanar ta kafar bidiyo. Taron da ya ba da damar tattauna dabarun hadin gwiwa, game da shawo kan kalubalen da ka iya biyo bayan wannan annoba.
A ranar 5 ga watan Yuni, kwana guda kafin taron dandalin CASCF, Mr. Liao ya mika kayan tallafin yaki da cutar ta COVID-19, wanda gwamnatin Sin ta samarwa kungiyar kasashen Larabawa mai helkwata a Masar. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China