Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta karfafawa kasashen Afirka gwiwa da su bunkasa alaka a fannin raya albarkatun ruwa
2019-07-22 20:04:29        cri

Jakadan kasar Sin a kasar Namibia Zhang Yiming, ya karfafawa kasashen Afirka gwiwa da su karfafa yin hadin gwiwa a bangaren rayawa da tsimin albarkatun ruwa, ta yadda za su magance matsalolin karancin ruwa da suke fuskanta.

Jakada Zhang Yiming ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi a taron dandalin ruwa na Sin da Afirka da ya gudana a Windhoek, yana mai cewa, matsalar karancin ruwa ta kasance babbar matsalar da ke shafar rayuwa da ci gaban bil-Adam.

Ya ce, dandalin zai zama wata gadar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da ma alaka tsakanin Sin da kasashen Afirka da bangarori daban-daban

Kasar Sin tana da kwarewa, albarkatu da fasahohi, abu mafi muhimmanci kuma, kasar Sin tana da niyya mai kyau na yin aiki tare da kasashen Afirka ta yadda bangarorin biyu za su amfana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China