Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kimanin bakin haure 1,000 aka ceto a gabar ruwan Libya a shekarar 2020
2020-01-15 11:19:40        cri

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya (IOM) ta bayyana a jiya Talata cewa, kimanin bakin haure 1,000 aka ceto a gabar ruwan Libya a shekarar 2020.

Hukumar ta ce, ma'aikatanta na wuraren da jiragen ruwa ke tsayawa don ba da taimako, sai dai hukumar ta nanata cewa, babu tabbas game da matakan kare rayukan bakin hauren da ma tabbacin tsaronsu.

A cewar hukumar IOM, a shekarar 2019 da ta gabata, sama da bakin haure 110,000 dake bi ta barauniyar hanya ne suka isa Turai ta Bahar Rum, yayin da mutane 1,283 suka mutu a hanya.

IOM ta sha jadadda cewa, bai dace ba bakin haure su rika yada zango a tashar ruwan Libya ba, saboda yadda yanayin tsaro ya tabarbare a kasar.

Libya dai ta zama wurin da bakin haure galibin 'yan Afirka ke yada zango, a kokarin da suke tsallaka Bahar Rum don shiga Turai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China