Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci kasashen duniya su tashi tsaye su yaki COVID-19
2020-07-04 15:55:31        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bukaci kasashen duniya da ke fama da cutar COVID-19, su tashi tsaye wajen shawo kan annobar, tare da dakile ci gaba da yaduwarta.

Kawo yanzu, cutar ta harbi mutane a kalla miliyan 11 tare da sanadin rayuka sama da 523,000 a fadin duniya. Kuma cutar ta fi kamari ne a nahiyar Amurka, inda aka fi samun yawan wadanda suka kamu tare da wadanda suka mutu, a kasar Amurka.

Hukumar ta kara da cewa, kasashe da dama na yin biris da abun da bayanai ke nunawa, tana mai cewa, har yanzu lokaci bai kure ba na dakile yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China