2020-07-06 15:27:16 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da martanin wasikar da cibiyar Butuka dake kasar Papua New Guinea ta aike gare shi, inda a cikin wasikar ya bayyana farin ciki, da jin cewa cibiyar ta shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, har ma ta koma gudanar da darussa kamar yadda aka saba. Xi ya ce Sin za ta ci gaba da taimakawa cibiyar, wajen cimma muradun ta na ba da ilimi.
Wasikar ta shugaba Xi, ta biyo bayan wadda cibiyar ta Butuka ta aika ne ga shugaban na Sin, inda a cikin ta, ta jinjinawa kulawar da yake nunawa ga bunkasar ta. Cibiyar ta kuma yabawa kasar Sin, game da gudummawar ta, ga bunkasar hadin gwiwar kasa da kasa, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China