Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin cimma sabbin nasarori ta amfani da gyare-gyare
2020-06-30 21:52:07        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin amfani da gyare gyare, wajen shawo kan sauyin da ake fuskanta a yanzu, tare da kara bude sabbin kudurori, baya ga fadada hangen sabbin dabaru, wadanda za su haifar da sakamako mai armashi a muhimman sassa.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar Sin, ya lasafta wadannan fannoni ne, cikin jawabinsa na yau Talata, yayin taro na 14, na kwamitin koli dake lura da ayyukan zurfafa sauye sauye, da gudanar da cikakken garanbawul. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China