2020-07-01 21:51:26 cri |
Cikin shekaru 99 da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke kokarin gudanar da harkoki masu alaka da mulki a kasar Sin, ta dade tana fuskantar kalubaloli daban daban, musamman ma a fannin moriya da yadda ake fama da kwadayi a zuci. Matsalar cin hanci da karbar rashawa ta shafi wasu 'yan jam'iyyar, da jami'ai, lamarin da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.
Babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya taba bayyana cewa, "Kada a yi facaka da kudin jama'a. Kana kar a yi amfani da ikon gwamnati bisa dalilin son kai."
Yadda ake kokarin dakile cin hanci da rashawa a kasar Sin ya janyo hankalin mutanen duniya .
Yawan jami'an da aka kama su da laifin cin hanci da rashawa tsakanin shekarun 2017-2019
Manyan jami'ai na gwamnatin tsakiya
shekarar 2017 mutane 18
shekarar 2018 mutane 23
shekarar 2019 mutane 20
Manyan jami'an kamfanonin mallakar kasa
shekarar 2017 mutane 9
shekarar 2018 mutane 15
shekarar 2019 mutane 62
Jami'an gwamnatocin larduna
shekarar 2017 mutane 221
shekarar 2018 mutane 354
shekarar 2019 mutane 408
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China