Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

Kasar Sin ba ta taba raba ci gabanta daga ci gaban duniya ba. Tana sauke nauyin dake bisa wuyanta, a matsayin wata babbar kasa, bisa tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama.

Marigayi Mao Zedong wanda ya kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin ya taba cewa, kamata ya yi kasar Sin ta kara ba da gudummawa wajen ci gaban 'yan Adam.

Marigayi Deng Xiaoping, wanda ya tsara manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare ya taba cewa, ya zuwa shekaru 2050 da shekaru 2060, karfin kasar Sin na gurguzu, da rawar da za ta taka za ta sha bamban sosai, don haka za ta kara ba da gudummawa ga bil'Adama.

Xi Jinping wanda yake jagorantar kasar Sin a sabon zamani ya ce, har kullum, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana mayar da kara ba da sabuwar gudummawa ga bil Adam a matsayin aikinta.

Xi Jinping: aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa, kyakkyawar hanya ce da kasar Sin take bi wajen yin amfani da dama, da neman ci gaba cikin hadin gwiwar kasa da kasa.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China