An kafa dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong ba domin neman cin zarafin 'yan adawa dake yankin ba
Mataimakin darekta mai kula da harkokin Hong Kong da Macau na majalisar gudanarwar kasar Sin, mista Zhang Xiaoming, ya furta a yau Laraba, a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin cewa, dalilin da ya sa aka kafa dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong na kasar Sin, shi ne neman hukunta 'yan tsirarrun mutane da suke karya doka, da lalata tsaron kasa, maimakon mai da 'yan adawa dake yankin abokan gaba, ko kuma neman cin zarafinsu.
Babban makasudin dokar, a cewar mista Zhang, shi ne tabbatar da tsaron kasar Sin, da samun kwanciyar hankali a yankin Hong Kong, da dorewar tsarin "kasa daya mai tsarin mulki iri 2". (Bello Wang)