Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawancin kasashe sun amince da matakin kasar Sin na tabbatar da tsaron kasa
2020-07-01 19:45:50        cri
A kwanan baya, wasu kasashen yammacin duniya sun tabo maganar kafuwar dokar tsaron kasa da ta shafi yankin Hong Kong na kasar Sin, a taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD. Sai dai a wajen taron wasu kasashe fiye da 50, sun gabatar da wani jawabi na bai daya, inda suka nuna kin amincewarsu kan shisshigin da kasashen yamma suke yi wa harkokin gidan kasar Sin, tare da nuna goyon baya ga kasar Sin, kan yadda take kokarin daidaita al'amura a yankin Hong Kong.

Dangane da haka, Zhao Lijian, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Laraba cewa, yawancin kasashen duniya sun yarda da mataki mai dacewa da kasar Sin ta dauka, kuma hakan ya nuna cewa, ba za a iya yin watsi da adalci a duniya ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China