Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar Sin dake MDD ta karyata ra'ayin wakilin Amurka game da Sin
2020-07-01 11:49:30        cri
Kakakin tawagar kasar Sin dake MDD ya bayar da sanarwa a jiya Laraba 30 ga watan Yuni, inda ya karyata ra'ayin zaunannen wakilin Amurka dake majalisar game da Sin ba tare da kwakkwarar hujja ba.

Sanarwar ta bayyana cewa, a kasar Sin mai fadin muraba'in kilomita miliyan 9 da dubu 600, jama'ar kasar suna rayu cikin zaman lafiya da jin dadi da kuma yanci, sannan babu yake-yake, da asarar gidaje, da jin wani tsoro. Wannan ya shaida yanayin kare hakkin dan Adam a kasar Sin, kana ya shaida gudummawar da Sin ta samar wa duniya kan sha'anin kiyaye hakkin dan Adam. A halin yanzu, ya kamata kasashen duniya su mayar da hankali ga yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Amurka. Sin tana kashedi ga kasar Amurka da ta yi la'akari da matsalolin dake damun ta.

Sanarwar ta kara da cewa, Sin ta himmatu wajen kare muradunta da nuna adawa da tsoma baki a harkokinta da kasashen waje suke yi, da kuma sa kaimi ga tabbatar da kare hakkin dan Adam. Duk wani yunkurin na zargin kasar Sin kan batun kare hakkin dan Adam da kuma siyasantar da batun ba zai yi nasara ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China