Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da hare-hare a Najeriya
2020-06-17 10:45:35        cri
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da hare-haren makon jiya, wanda 'yan ta'adda suka kaddamar a wasu sassan arewacin Najeriya, hare-haren da suka sabbaba rasuwar a kalla mutane 120.

Cikin wata sanarwa da suka fitar, mambobin kwamitin na tsaro, sun bayyana matukar tausayawa, tare da gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da su, da ma gwamnati da al'ummar kasar. Kaza lika sun yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Mambobin kwamitin tsaron sun kuma bayyana bukatar gano wadanda suka aikata hare-haren, da masu tsara su, da masu samar da kudade ko daukar nauyin ayyukan ta'addanci, don gurfanar da su gaban kuliya. Har ila yau sun bukaci daukacin jihohin kasar da su hada kai da gwamnatin tarayya, da ma dukkanin hukumomin da abun ya shafa, domin shawo kan wannan kalubale na tsaro.

Daga nan sai suka jaddada cewa, dukkanin wani nau'in ta'addanci da tasirinsa, na yin barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, don haka ya zama wajibi ga daukacin jihohin kasar, su aiwatar da matakan dakile barazanar 'yan ta'adda ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China