Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
EU ta amince da yarjejeniyar ficewar Birtaniya
2020-01-31 16:46:06        cri
Tarayyar Turai EU, ta amince da kammala yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga tarayyar.

Sanarwar da tarayyar ta fitar, ta ce wannan matakin na zuwa ne, rana guda bayan zaman majalisar dokokinta, ta amince da yarjejeniyar ficewar Birtaniya da kuri'u 621, yayin da aka samu kuri'un kin amincewa 49 da 13 da suka kaurcewa kada kuri'ar.

Dukkan shugabannin EU da Birtaniya sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda ta ba da damar janyewar Birtaniya daga tarayya. Yarjejeniyar za ta fara aiki ne bayan Birtaniya ta janye daga EU yau da daddare, wadda za ta kawo karshen shekaru 47 da ta shafe a matsayin mambar tarayyar.

Daga ranar 1 ga watan Fabreru, Birtaniya ba za ta sake kasancewa mambar EU ba, duk da cewa za ta ci gaba da amfani da dokokin EU har zuwa lokacin da za ta kammala janyewa a karshen shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China