Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin Watsa Labaran Ketare: Matakan Birnin Beijing Na Dalike Yaduwar COVID-19 Za Su Zama Abin Koyi
2020-06-24 13:03:45        cri
Tun lokacin da aka gano sabbin masu dauke da cutar COVID-19 a birnin Beijing a ranar 12 ga watan nan, kasashen duniya suka fara mai da hankali kan wannan annoba a birnin.

A ranar 19 ga wata, jaridar The New York Times ta yada labarai game da yadda birnin ke tinkarar wannan annoba. Inda jaridar ta ce an dauki matakai yadda ya kamata, tun lokacin da aka gano mai dauke da cutar a Beijing, domin magance bazuwar ta cikin gaggawa.

Haka kuma, jaridar ta ce, gwamnatin birnin Bejing, ta tsaida kudurin gaggawa na rufe kasuwar Xinfadi, wadda ta kasance wurin da aka fara gano cutar, sa'an nan, ta killace gine-gine sama da guda 40 dake kewayen wannan kasuwa.

Daga ranar 11 zuwa ranar 22 ga wata, an samu mutane 249 da aka tabbatar sun kamu da cutar a birnin Beijing, amma, a wannan karo, ba a killace birnin baki daya ba, sai dai an dauki matakan kandagarki a matsayin koli, a wuraren da suka fi fama da matsalar yaduwar cutar.

Hakan ya sa, wasu kantuna, da dakunan cin abinci, da dakunan gyaran gashi suke ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba, kuma al'ummomin birnin su ma ba su dakatar da ayyukansu ba.

Jaridar New York Times ta kuma bayyana cewa, birnin Beijing ya dauki wadannan matakai ne bisa fasahohin da kasar Sin ta samu, na yaki da cutar a watanni da dama da suka gabata.

Ta kuma ce idan aka cimma nasarar dakile yaduwar cutar a birnin na Beijing, wadannan matakai za su kasance abun koyi ga kasashe daban daban, inda tuni wasu kwararrun kasa da kasa da dama suka nuna amincewa da hakan.

Bisa labarin da jaridar South China Morning Post(SCMP) ta fidda, a lokacin da wasu kasashen Asiya suke son farfado da tattalin arzikinsu, za su gamu da matsalar sake dawowar cutar COVID-19. Shi ya sa, matakan da aka dauka a birnin Beijing za su zama abin koyi gare su. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China