![]() |
|
2020-06-24 11:28:27 cri |
Cikin sharhin, gidan rediyon ABC ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar matsalar sake yaduwar cutar COVID-19, birnin Beijing bai bata lokacinsa ba wajen tsayar da yaduwar cutar. Cikin wannan birni mai kunshe da mutane sama da miliyan 20, ana gudanar da aikin dakile yaduwar annoba cikin unguwanni yadda ya kamata, yayin da kuma ake yin gwajin cutar cikin sauri. Daga ranar 11 ga wata, an yi gwajin cutar har sau miliyan 3.5 kan mazauna wurin cikin kwanaki 12.
Ban da haka kuma, ya ce, ba a killace birnin Beijing ba, mutane suna iya fita birnin, bayan sun yi gwajin cutar dake tabbatar da cewa, ba su dauke da ita. Kuma domin farfadowar tattalin arziki, ba a rufe dukkanin dakunan ci abinci na birnin Beijing ba, sai dai yin musu bincike. Haka kuma, an jinkirta lokacin bude makarantu, da lokacin dawowar bakin aiki a fannonin motsa jiki da nishadantarwa, domin dukufa wajen dakile yaduwar cutar COVID-19.
A sa'i daya kuma, ana ci gaba da samun karin masu dauke da cutar, da adadinsu ya kai sama da goma a kowace rana cikin kwanaki 7 da suka gabata a birnin Melbourne. Shi ya sa, gidan rediyon ABC na kasar Australia na fatan birnin Melbourne zai iya koyon fasahohin birnin Beijing, domin magance dawowar cutar COVID-19. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China