![]() |
|
2020-06-18 13:13:58 cri |
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da Ministan harkokin waje da cinikin kasa da kasa na Zimbabwe Sibusiso Moyo, sun halarci taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 ta kafar bidiyo a fadar shugaban kasa. Bayan taron, Sibusiso Moyo ya bayyana cewa, taron na wannan karo ya nuna ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da cutar COVID-19.
Ya ce, kasar Sin ta nuna fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya, domin bada taimako ga kasashen Afirka wajen yin kandagarki da dakile yaduwar cutuka. Lamarin da zai bada tallafi ga kasarsa da ma sauran kasashen Afirka, da kuma taimaka musu wajen kyautata ayyukan kiwon lafiya. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China