![]() |
|
2020-06-12 16:00:43 cri |
Kuma bi da bi, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirkan sun isa kasashen nahiyar.
A ranar 11 ga wata, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasar Sudan ta Kudu sun isa birnin Juba, fadar mulkin kasar. Wadannan kayayyakin yaki da cutar sun hada da kayan ba da kariya, da abun rufe hanci da baki, da kuma maganin tantance cutar numfashi ta COVID-19 da sauransu. Wannan shi ne kayayyaki karo na hudu, da kasar Sin ta baiwa kasar Sudan ta Kudu tun daga watan Maris na bana.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu Mayen Dut Wol, ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin, dangane da taimakon da ta baiwa gwamnati da al'ummomin kasar Sudan ta Kudu.
A daren ranar 10 ga wata kuma, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasar Mauritania sun isa kasar. A yayin bikin mika kayayyakin, wani jami'in kasar Mauritania ya bayyana cewa, taimakon da kasar Sin ta baiwa kasar sa, ya nuna kyakyyawan zumunci da hadin gwiwa mai dorewa dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China