Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kolin Sin da Afirka muhimmin hadin gwiwa ne a yaki da COVID-19
2020-06-18 10:00:23        cri

Babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce taron kolin Sin da Afrika wani muhimmin dandali ne wajen karfafa hadin gwiwa don yaki da annobar COVID-19.

Jami'in ya ce, tun bayan barkewar annobar, Sin tana cigaba da taimakawa Afrika, musamman tura tawagar kwararrun masana kiwon lafiya, da yin musayar bayanai, bugu da kari, da samar da kayan tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen.

Tedros da Antonio Guterres, babban sakataren MDD, sun halarci taron kolin na Sin da Afrika ta kafar bidiyo a ranar Laraba, a matsayin baki na musamman.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China