Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: kasar Sin na adawa da siyasantar da annobar COVID-19 da nuna wariyar launin fata
2020-06-17 23:56:57        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a yayin taron kolin Sin da Afirka na musamman kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 da aka shirya a yau Laraba, cewa ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su tsaya kan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da adawa da siyasantar da annobar COVID-19, da alakanta annobar da wata kasa, kana da adawa da nuna wariyar launin fata da son zuciya, da kuma tsayawa kan nuna daidaito da adalci a duniya.

Ya kara bayyana cewa, kasarsa na fatan hada kai tare da bangaren Afirka, don kiyaye tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, da nuna goyon baya ga kungiyar WHO don kara ba da gudummowa kan yaki da annobar, da kiyaye babbar moriyar bai daya ta kasar Sin da kasashen Afirka da ma daukancin kasashe masu tasowa, da kuma ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China