2020-06-16 11:11:00 cri |
Kasar Sin, da kasar Afirka ta Kudu mai shugabancin kungiyar AU a wannan karo, da kuma kasar Senegal wadda kasa ce da ta shugabanci dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, sun yi kira da a gudanar da taron ta kafar bidiyo, inda shugabannin kasashe membobin tawagar shugabancin taron koli na kungiyar AU, da kasashe masu shugabancin manyan kungiyoyin yankunan nahiyar Afirka da sauransu da kuma shugaban kwamitin kungiyar AU za su halarci taron. Hakazalika kuma, babban sakataren MDD, da babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya su ma za su halarci taron bisa gayyatar musamman da aka yi musu. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China