2020-06-12 10:34:34 cri |
Shugaban Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Philippine Rodrigo Duterte. A yayin tattaunawar, Xi ya ce irin wannan yunkuri, zai taimakawa kasashen biyu, cimma nasarar bunkasa fannonin su na zamantakewar al'umma, da tattalin arziki, ta yadda al'ummun su za su ci gajiya.
A wani ci gaban kuma, shugaban na Sin, ya yi kira da a zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar sa da Belarus. Shugaban ya yi wannan kira ne yayin zantawa ta wayar tarho da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko a daren jiya Alhamis.
Xi Jinping ya shawarci sassan biyu, da su yi kokari tare, wajen sauya kalubalen dake addabar su zuwa damammaki, su kuma zurfafa hadin gwiwa wajen cimma nasarar shawarar ziri daya da hanya daya. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China