Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kasashen dake gabas ta tsakiya da arewacin Afirka za su bude aikin yawon shakatawa
2020-06-13 16:10:27        cri
Wasu kasashen dake yankunan gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, sun sanar a jiya cewa, suna shirin sake bude aikin yawon shakatawa, gami da sassauta matakan kandagarkin cuta da suka shafi zaman rayuwar jama'a.

Ma'aikatar aikin yawon shakatawa ta kasar Masar ta ce, an riga an ba da izinin bude kofa ga wasu otel-otel 232, wadanda za su iya bude rabin dakunansu don karbar baki. sa'an nan za a farfado da ayyukan zirga-zirgar jiragen sama da yawon bude ido, a wasu jihohin kasar, inda masu kamuwa da cutar COVID-19 ba su yi yawa sosai ba.

A nata bangare, kasar Tunisia ta sanar da bude kan iyakarta daga ranar 27 ga wata, don karbar baki masu yawon bude ido na kasashen waje. Sai dai za a bukace su gabatar da sakamakonsu na gwajin cutar COVID-19.

Yayin da a kasar Saudiya, aka ce za a maido da aikin horo da gasannin motsa jiki, daga ranar 21 ga wata. Sai dai har yanzu, ba a ba da damar zuwa kallon gasannin a filayen wasa ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China