2020-02-26 19:34:11 cri |
Mahukuntan kasar Sin, sun bayyana matukar alhini game da rasuwar tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak. Yayin wani taron ganawa da menema labarai da ya gudana a Larabar nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, a madadin kasar Sin, ya mika sakon ta'aziyyar Sin ga iyalan marigayin.
Zhao Lijian ya ce tsohon shugaba Mubarak, ya ba da gagarumar gudummawa, wajen bunkasa kawance tsakanin Sin da Masar. Don haka gwamnatin Sin, da daukacin al'ummar Sinawa, ba za su taba mantawa da gudummawarsa ba.
Ya ce Sin za ta yi aiki tare da Masar, domin kara zurfafa cikakkiyar dangantaka bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni dake tsakanin kasashen biyu. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China