2020-06-09 20:24:47 cri |
Kauyen Hongde da ke yankin Hongsipu a birnin Wuzhong, shi ne wuri na farko da Xi Jinping ya ziyarta, kuma akwai iyalai 1699 da suka kunshi mutane 7013, kuma yawancinsu sun kaura zuwa kauyen ne daga wasu wurare. A shekarar bara, dukkan mazauna kauyen sun fita daga kangin talauci.
Sashen Rawayen kogi a birnin Wuzhong, shi ne wuri na biyu da Xi Jinping ya ziyarta a wannan rana, inda ya kara fahimtar yadda ake kiyaye muhallin halittu a kogin.
Haka zalika, Xi Jinping ya ziyarci unguwar Jinhuayuan a garin Jinxing da ke gundumar Litong a Wuzhong. A shekarar bara, an zabi unguwar a matsayin abin koyi a fannin hada kan kabilu daban daban a kasar. A yayin da yake unguwar, Xi Jinping ya ce, dukkan kabilu al'ummar kasar Sin ne, kuma ba yadda za a yi kasa ta rayu ba tare da yaki da talauci da samar da al'umma mai wadata ta kowacce fuska da kuma wayewa ba. Dukkan al'umma na aiki ne kafada-da-kafada, wanda yake nuna shekaru dubu 5 na wayewar kan Sinawa da karfin tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China