Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi:Alakar Sin da Myanmar tana gaba mai muhimmanci da ta hade lokutan baya da ma nan gaba
2020-06-08 21:00:37        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, yayin da duniya ke fuskantar wasu sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, alakar kasarsa da Myanmar a halin yanzu tana wani muhimmin gaba wadda ta gaji abubuwa a baya tare da shiga wani sabon zamani a nan gaba,.

Xi ya bayyana haka ne, Litinin din nan, yayin da yake musayar sakonnin fatan alheri da taya murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashe da takwaransa na kasar Myanmar U Win Myint. Yana mai cewa, a shirye yake ya yi aiki da Win Myint, don kara yaukaka alakar dake tsakaninsu, don ganin sun gina al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Myanmar ta yadda al'ummomin sassan biyu, za su kasance makwabta da abokai da abokan hulda na gari har a abada. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China