Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da EU da Jamus domin samarwa duniya tabbaci
2020-06-04 11:49:44        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a ranar Laraba cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Jamus da kungiyar tarayyar Turai EU wajen karfafa hadin gwiwa, da aiwatar da cudanyar bangarori daban daban, da warware kalubalolin dake addabar kasa da kasa, da kuma hada karfi da karfe wajen samar da makoma game da halin rashin tabbas da duniya ke fuskanta.

A tattaunawar da ya yi ta wayar tarho tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, Xi ya ce gwamnatin Sin a shirye take ta yi aiki da Jamus wajen goyon bayan ayyukan hukumar lafiya ta duniya WHO, wajen daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa karkashin tsarin MDD da kungiyar G20, domin taimakawa kasashen Afrika wajen yaki da annobar COVID-19, da kuma bada taimako wajen ceto fannin tsaron kiwon lafiya na kasa da kasa.

A nata bangaren, Merkel ta ce Jamus ta yi matukar farin ciki da sanarwar da shugaba Xi ya bayar cewa rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin za ta samar zai kasance mai matukar amfani ga fannin kiwon lafiyar kasa da kasa. Ta kara da cewa, Jamus, tana fatan za ta cigaba da tattaunawa da bangaren kasar Sin domin aiwatar da muhimman ajandoji karkashin hadin gwiwar Jamus da Sin da kuma EU da Sin da ingiza matsayin ci gaban dangantakar dake tsakanin Jamus da kasar Sin da kuma EU da Sin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China