Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta Sin za ta fadada sadarwar 4G a kauyuka masu fama da talauci
2020-03-16 09:51:10        cri
Jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, za ta zuba sama da yuan miliyan 330, kwatankwacin dala miliyan 47, wajen gina tasoshin samar da tsarin sadarwar 4G ga kauyuka 334 dake fama da talauci.

Idan aka kammala, kauyukan za su samu hanyoyin sadarwar intanet irin wadanda ake jonawa da waya da kuma wanda ba ya bukatar waya.

Yayin da Xinjiang ke da dimbin filaye da rashin yawan jama'a, kauyukanta, musammam masu fama da talauci, ba su da hanyoyin sufuri da na sadarwa masu kyau, kuma ingancin tsarukansu na sadarwar 4G da na broadband mai matukar sauri, ba su kai na sauran larduna da yankunan kasar Sin ba.

A bana, jihar Xinjiang, za ta tabbatar da samar da ingantattun tsarukan sadarwa a yankuna masu fama da talauci, a wani yunkuri na fitar da kauyukan daga kangin talauci.

A cewar hukumar yada labarai ta yankin, har ila yau, jihar za ta ci gaba da ba da tallafi da inganta amfani da lantarki da samun labarai, ta yadda manoma da makiyaya za su ci gajiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China