Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin sun dudduba tare da tattaunawa kan daftarin kundin dokar da ya shafi zaman al'umma
2020-05-25 14:27:53        cri

Manyan kusoshin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), da shugabannin gwamnatin kasar, a ranar Lahadi sun gana tare da 'yan majalisar wakilan jama'ar kasa da wakilan majalisar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, inda suka duba tare da tattaunawa kan daftarin kundin dokar da ya shafi zaman al'umma a lokacin taron shekara shekara na majalisun biyu na bana.

Dokar ta shafi batun kai dauki domin dakile annobar COVID-19, da samar da doka daga bangaren shari'a da za ta bayar da cikakken goyon baya kan tsarin gwamnati na kai daukin yaki da annobar COVID-19 da dakile cutar.

Yayin da kasashe mafiya yawa na duniya suke da dokokin da suka shafi zaman al'umma, amma kasashen 'yan kalilan ne suke tsara kundin dokar, a cewar shugabannin, sun kara da cewa, daftarin kundin dokar ba kawai yana alamta sabon cigaban da fannin dokokin kasar Sin ya samu ba ne, har ma yana bayar da gudunmowa game da hikimomin Sinawa da matakan da suke amfani da su wajen bunkasa cigaban kasa da kasa wajen gina dokoki.

An samu ra'ayoyi masu tarin yawa da aka bayyana daga fannoni daban daban a lokacin harhada daftarin kundin dokar, a cewar shugabannin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China