Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci taron wakilan lardin Hubei
2020-05-25 13:38:38        cri

A yammacin jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron wakilan lardin Hubei na NPC. Yayin zaman shugaba Xi ya ce, "Ina ganin cewa, dole na halarci taron wakilan lardin Hubei, saboda ku wakilci mazaunen Hubei da yawansu ya kai miliyan 60, ina gai da ku."

Mai ba da jawabi na farko shi ne darektan kwamitin JKS, na asibitin Taihe dake birnin Shiyan na lardin Hubei Luo Jie. Bayan gabatar da jawabin sa, shugaba Xi ya ce, labarin da ya gabatar game da jiyyar tsoho mai shekaru 87 a duniya ya burge shi matuka.

Bayan da wakilan suka kammala jawabansu, shugaba Xi ya sake gai da su, da kuma nuna godiya gare su. Ya ce, barkewar wannan cuta ta COVID-19, ya jarrabawa tsarin daidaita ayyuka a wurare daban-daban. Musamman ma a unguwanni, da kauyuka, da garuruwa. Ya ce an kai ga samar da fasahohi, da kuma ci gaba da aka samu a wannan fanni, don kara himma, da kuma kyautata ayyuka. Ya ce, aikin dake gaban lardin Hubei cikin gaggawa shi ne, kandagarkin cutar, da raya tattalin arziki da al'umma.

Cikin muhimman abubuwa da shugaban ya tattauna a taron wakilan Hubei, akwai batun yadda za a yi kandagarki, da kuma magance matsalar kiwo lafiya cikin gaggawa, da kuma yadda za a kafa tsarin kiwon lafiya a dukkanin fadin al'umma. A cewarsa, kamata ya yi a kara ilmi bayan barkewar wani bala'i.. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China