Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi gargadi game da amfani da hydroxchloroquine kan COVID-19
2020-05-21 10:10:04        cri
Darekta a hukumar lafiya ta duniya (WHO) mai kula da ayyukan lafiya na gaggawa Dr. Micheal Ryan, ya gargadi jama'a da su guji amfani da maganin hydroxchloroquine ko Chloroquine, magungunan da ake amfani da su wajen warkar da zazzabin cizon saura na malariya ko wasu cututtuka wajen maganin COVID-19, ba tare da iznin masana lafiya ba.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai kan tambayar da aka yi masa, game da yadda ake amfani da wadannan magunguna wajen warkar da masu fama da COVID-19 a wasu kasashe, Dr Ryan ya ce, duk da cewa, ana amfani da wadannan magunguna kan wasu cututtuka da dama, a wannan gaba, har yanzu ba a gano cewa, za a yi amfani da su wajen warkar da cutar COVID-19, ko maganin Prophylaxis wajen rage kaifin cutar ba.

Ita ma jagorar shirin ayyukan lafiya na gaggawa Dr Maria Kerkhove, ta bayyana cewa, ya zuwa wannan lokaci, akwai marasa lafiya sama da dubu uku da aka zabo daga asibitoci 320 a kasashe 17, kuma wannan ya nuna cewa, sun amince a gwada maganin a jikinsu, hakan ya nuna hadin gwiwa da niyyar hada kai don cimma manufa guda ta hanyar gano tsarin jinyar da ya fi tasiri da inganci kan COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China