Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudurin taron hukumar WHO ya shaida ra'ayinta game da batun yankin Taiwan
2020-05-20 14:28:18        cri

A gun taron hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO karo na 73 da aka gudanar a ranar 18 ga wannan wata, an sanar da cewa, ba a tattauna daftarin gayyatar yankin Taiwan don halartar taron hukumar WHO a matsayin 'yar kallo ba. Game da batun, kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin Ma Xiaoguang ya bayyana a jiya cewa, wannan kuduri ya sake shaida cewa, yunkurin samun 'yancin kan yankin Taiwan ba shi da tushe, haka kuma taron bai goyi batun yankin Taiwan ba, kasa da kasa sun amince da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

An gudanar da taron hukumar WHO na wannan karo a yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 a duniya, don haka aka rage tsawon lokacin gudanar da taron zuwa kwanaki biyu. Ya kamata a yi amfani da wannan gajeren lokaci don tattauna yadda za a yi hadin gwiwa wajen tinkarar cutar COVID-19, hukumar jam'iyyar DPP ta yankin Taiwan ta yi amfani da wannan lokaci wajen bayyana ra'ayin neman 'yancin kan yankin Taiwan, da yunkurin shigar da siyasa cikin kwararriyar hukumar kasa da kasa kamar WHO, babu shakka wannan ra'ayi zai gamu da adawa daga al'ummomin kasashen duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China