2020-05-14 14:33:59 cri |
Jiya Laraba, WHO ta kira taron manema labarai a birnin Geneva game da cutar numfashi ta COVID-19. Yayin taron, jami'i mai kula da halin gaggawa na hukumar Michael Ryan ya nuna cewa, cutar COVID-19 za ta zama wata matsala ta dogon lokaci, kuma har yanzu ba a san yaushe ne za a dakile ta baki daya ba, kana mai yiwuwa ne za ta zama wata annoba da ba za ta bace a duniya ba.
Michael Ryan ya ba da misali da cewa, cutar sida ba ta bace ba, amma yanzu an fitar da matakin jiyya da kuma kandagarkin ta, kana Bil Adama ba ya tsoron wannan cuta kamar yadda ya yi a baya.
Amma duk da haka, jami'in ya yi fatan za a kai ga kirkiro allurar rigakafi mai matukar amfani, kuma a rarraba ta ga dukkanin al'ummun duniya. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China