![]() |
|
2020-05-19 20:40:37 cri |
Don gane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Talata cewa, wannan ya sake shaida cewa, yunkurin neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin ba zai yi nasara ba. Kana yadda ake neman tsoma batun Taiwan cikin abubuwan da aka tattauna a babban taron hukumar WHO, ba zai samu goyo baya daga al'ummun duniya ba.
Zhao ya ce, mambobin hukumar WHO suna tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da bin wasu kudirorin da babban zauren MDD, da na hukumar WHO suka zartas, da kokarin tabbatar da adalci a harkokin duniya, don haka kasar Sin na matukar jinjina musu. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China