Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar siyasa ta kwamitin koli na CPC ta kira taron tattauna rahoton aikin gwamnati
2020-05-15 20:32:49        cri
A yau ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kasar Xi Jinping, ya jagoranci taron hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, don tattauna daftarin rahoton aikin gwamnati, wanda majalisar zartaswa za ta mikawa zama na 3 na majalisar wakilan jama'a (NPC) karo na 13 don tattaunawa a kai.

Taron ya kuma jaddada cewa, halin da duniya ke ciki game da COVID-19 da yanayin tattalin arzkin duniya sun kasance abin damuwa da sarkakiya. A hannu guda kuma kasar Sin tana fuskantar kalubale da ba ta taba gani ba a ci gaban da ta samu.

A cewar taron, idan har ana bukatar kwalliya ta biya kudin sabulu a aikin gwamnati a wannan shekara, akwai bukatar a mayar da hankali kan manufar da ake fatan cimmawa da aikin kammala gina al'umma mai matsakacin wadata daga dukkan fannoni, da kara zage damtse wajen inganta matakan kandagarki da hana yaduwar COVID-19 da ci gaban al'umma, da nacewa kan abin da aka sanya a gaba, da tabbatar da cewa, an cimma nasarar yaki da talauci, ta yadda za a kammala gina al'umma mai matsakacin wadata a dukkan fannoni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China