Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing ta zo ta bakwai a tsakanin biranen Asiya da tekun Pasifik wajen karbar bakuncin tarukan kasa da kasa
2019-08-29 11:39:51        cri
A shekarar 2018, yawan tarukan kasa da kasa da birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin ta karbi bakuncinsu ya kai 94, adadin da ya karu da kaso 13.8% bisa makamancin lokacin bara, lamarin da ya sa ya zama na bakwai a tsakanin biranen yankin Asiya da tekun Pasifik da ma na farko a kasar Sin.

A shekarun baya bayan nan, an yi ta gudanar da tarukan kasa da kasa a nan birnin Beijing, tarukan da suka fi shafar fannonin kiwon lafiya da zaman al'umma da nazarin kimiyya da fasahohin sadarwa da sauransu.

Alkaluman sun nuna cewa, a halin yanzu, akwai otel otel masu taurari biyar 61 a birnin Beijing, a yayin da otel-otel masu taurari hudu sun kai 114, kuma otel-otel da suka samu makin taurari sun kai dubu 98 a duk fadin birnin na Beijing. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China