![]() |
|
2020-05-11 13:04:32 cri |
Tawagar kwararrun masana kiwon lafiya masu yaki da annobar numfashi ta COVID-19 wadanda kasar Sin ta tura zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso a watan Afrilu sun kammala muhimmin aikinsu a kasashen biyu a kwanan nan, daga nan sun wuce zuwa kasashen Djibouti da Côte d' Ivoire.
A ranar 10 ga watan Mayu, firaministan Djibouti Abdoulkader Kamil Mohamed ya mika kyautar ranar samun 'yancin kan kasar ga kwararrun masana kiwon lafiya na kasar Sin su 12.
Tawagar kwararrun masana lafiyar na kasar Sin sun yi musayar kwarewa da kasashen Afrika da kuma ba da taimako, lamarin da ya kara zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika kana ya karawa kasashen Afrika kwarin gwiwar yaki da annobar COVID-19.
A lokaci guda, kokarin hadin gwiwar da Sinawa mazauna kasashen Afrika ke yi da takwarorinsu 'yan kasashen Afrika dake zaune a kasar Sin don yaki da annobar COVID-19 yana kara daga martabar abota dake tsakanin Sin da Afrika.
Gabonese J. Christian Nzengue, wanda ya shafe shekaru 17 yana aikin liikita a Guangzhou, ya mayar da martani game da kalaman da wasu kafafen yada labaran yammacin duniya ke yi game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, inda ya ce manufofin yaki da annobar COVID-19 da kasar Sin ke gudanarwa ba sa nuna bambanci a tsakanin kasashen duniya, ko bambancin kabila, kuma kasar Sin tana tafiyar da manufofinta na bai daya ne, tana kare kowa yadda ya kamata.
A kasar Mauritius, Lin Haiyan, shugaban kungiyar Mauritius Chinatown Foundation, ya tsara shirin wayar da kai ta intanet, inda ya gayyaci jami'ai daga ma'aikatar lafiya, da kwararru da masana daga kasashe masu yawa domin yin musayar kwarewa game da matakan kandagarki da yaki da annobar, da kuma tattauna yadda za'a yi hadin gwiwa wajen yaki da annobar da farfadowar ci gaban tattalin arziki cikin hanzari. Haka zalika ya ziyarci wasu kananan makarantu domin gabatar musu da matakan kandagarki da yaki da annobar ta COVID-19 ga dalibai. A lokacin da aka zartar da dokar zaman gida a kasar Mauritius, Lin Haiyan ya aika tallafin abinci ga wasu iyalai masu fama da talauci sama da 50.
A kasar Uganda, dake gabashin Afrika, an dakatar da aikin gina yankin Mbale na hadin gwiwar Sin da Uganda ta fuskar masana'antu sakamakon annobar COVID-19, kuma an samu babbar hasara. Zhang Zhigang wani Basinne da ke zauna a wurin da hadaddiyar kungiyar Sinawa da ke zaune a wurin sun bayar da tallafi ga ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Uganda da kayan abinci ga iyalai masu fama da talauci mazauna yankin Mbale.(By Ahmad Fagam daga CRI Hausa)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China