Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalisar koli ta addinin Iran: kasashen yammacin duniya sun fadi jarrabawar cutar COVID-19
2020-05-11 10:52:41        cri
Jiya Lahadi, shugaban majalisar koli ta addinin kasar Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya halarci taron hukumar ba da jagoranci kan ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta kasar ta kafar bidiyo. A yayin taron, ya gabatar da jawabi da cewa, kasashen yammacin duniya sun riga sun fadi jarrabawar yaki da cutar, don haka ya kamata a lura da kuma gudanar da bincike kan gazawarsu a fannin yaki da cutar.

Ya ce, kasashen Amurka da Turai ba su dauki matakan da suka dace ba, bayan barkewar cutar a sauran kasashen duniya a kalla da wata daya, har sai da cutar ta fara yaduwa a kasashen Amurka ta Turai, wato dai sun sami damar shiryawa yadda ya kamata, amma suka kasa. Ya ce ci gaban karuwar mutanen da suka kamu da cutar, da karuwar adadin rasuwar mutane, da kuma matsalar kasa samun ayyukan yi da al'ummomin kasashen suke fama da ita, dukkansu sun nuna cewa, wadannan kasashe ba su warware matsalar cutar COVID-19 yadda ya kamata ba.

Bugu da kari, ya yi Allah wadai da ra'ayoyin kasashen yammacin duniya, yana mai cewa, halayensu na kaunar kudade da kayayyaki, ya sa, ba su kula da tsoffafi, da masu fama da talauci da sauran mutane marasa karfi yadda ya kamata ba, wanda kuma hakan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa suka fadi jarrabawar cutar COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China