Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An canja lokacin da mutum na farko da ya kamu da cutar COVID-19 a kasashen Amurka da Faransa zuwa karshen rabin shekarar bara
2020-05-07 13:29:09        cri
Alkaluman kididdigar da hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai mutane 3,525,116 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya, yayin da mutane 243,540 suka mutu sanadiyyar wannan cuta. Kuma adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasashe ban da kasar Sin ya kai sama da miliyan 3.44. Kwanan baya, wani bincike ya nuna cewa, kasashe da dama sun yi saurin canja lokacin da mutum na farko da ya kamu da cutar ta COVID-19, shi ya sa, hukumar WHO ta yi kira ga kasa da kasa da su yi bincike kan wadanda suka kamu da cutar numfashi da wuri.

Gidan talabijin na CNN na kasar Amurka ya bada rahoton a jiya 5 ga wata cewa, masanan kasar Burtaniya sun gudanar da bincike kan wasu kwayoyin cutar da suka samu daga jikin mutane 7600 wadanda suka kamu da cutar COVID-19, kuma sakamakon binciken ya nuna cewa, wannan cuta ta fara yaduwa ne a kasashen duniya tun a karshen shekarar bara, kuma ta fara yaduwa da sauri bayan samun mutum na farko da ya kamu da cutar.

Haka kuma gidan talabijin na CNN ya bayar da rahoton cewa, wani likita dake aiki a wani asibitin dake birnin Paris na kasar Faransa ya bayyana cewa, sun samu sabbin shaidu dake nuna cewa, wani mutum ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a karshen watan Disamba na shekarar 2019. Idan har wannan labara ya tabbata, hakan na nuna cewa, wannan cuta ta fara yaduwa tun daga karshen watan Disamba na shekarar 2019 a kasar Faransa, kuma wannan cuta ta fara yaduwa a kasar Faransa, wata guda daya da wuri, idan aka kwatanta da lokacin da gwamnatin kasar Faransa ta sanar da mutum na farko da ya kamu da cutar, wato ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2020.

Bugu da kari, rahotannin da kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka fitar, sun nuna cewa, magajin garin birnin Belleville na jihar New Jersey Michael Melham ya bayyana a ranar 30 ga watan Afrilu cewa, ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a watan Nuwamba na shekarar 2019. Kuma sakamakon binciken da aka yi masa, ya nuna cewa, yana da kariyar cutar COVID-19 a jikinsa.

A jiya ne kuma, Kakakin hukumar WHO Christian Lindmayer ya bayyana cikin taron bayanin cutar COVID-19 da hukumar ta gabatar a birnin Geneva cewa, bayanai game da kasar Faransa ya canja ra'ayi kan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 baki daya. Don haka, ya yi kira ga kasa da kasa da su sake yin bincike kan samfuran kwayar cutar numfashi da ba su tabbatar da irin su ba, wadanda suka samu a bara, sabo da zai samar da sabbin bayanai da kuma kara fahimtar al'ummomin kasa da kasa kan wannan cuta. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China